Saturday, May 6, 2023

INA MUKA DOSA MATASA

 Na dade Ina tuntuntuni akan rayuwar wasu daga cikin matasa idan na tsaya nai tsumm sai na tambayi kaina amma amsar bata zoba wait shin: matasa rashin ilimi ne? Ko  rashin aikin yi? Shan miyagun kwayoti ne? Ko tabin kwakwalwa ne? Me muka dau rayuwa ne? 


Haka rayuwa zata kansan ce Kara zube ba mafadi, daga sace-sace, kwacen waya da raunata mutane, zambo cikin aminci abun har ya koma kashe mahaifa, na yi takaici a ce wai d'a ne zai kashe mahaifiyarsa, innalillahi wa inna ilaihi raji'un !


To Ina imanummu yake ina tauyawa da uwa da danta suke yi wa junansu? Uwar da ta dauki cikinka har tsahon wata tara ta haifeka ta shayar da kai ba irin wahalhalu da ba ta yi a kanka ba har ka girma, amma abun takaici irin sakamakon da zai saka mata da shi kenan wallahi mu bi duniya a sannu.


Ya Hayyu Ya Qayyum Allah ka karemu daga aikin danasani.

Friday, May 5, 2023

NASIHA

 Karka damu da idda Allah ya ajeka a rayuwa ka yadda da abun da Allah ya raba ya baka, kowanne mutum da kaddarar da Allah ya nufa agareshi ka yi amfani da iya abun ka suma ka yi rayuwarka cikin kwanciyar hankali.

Idan ka dorawa kanka sai abunda wane yayi zaka yi lalle ka hada kanka da wahala.Wasu su na bam mamaki wai sai rigar da wane  ya sa irinta lalle zasu sa, shin in tambayeka dan uwa Samunka da nasa daya ne ? ka yiwa kanka karatun ta nutsu ka zamo mai godiyar Allah a duk inda ka tsinci kanka.

 Ni Umar Usaini Kawon Kudu, Alhamdulillah na gode wa Allah, Allah ka kara Mana lafiya da wadatuwar arziki saboda Rasulillah Sallallahu alaihi wasallam, Amin ya Allah,🤲🤲🤲.



Sunday, April 23, 2023

BBD ALHERI NE

 A zahirin gaskiya ban taba ganin mutum mai san cigaban al' ummah irin Hon. Aminu Umar Farouk BBD irn temakon marayu da yake fa temakon talakawa masa karfi. Hakika BBD ALHERI NE.

Wednesday, September 2, 2020

MUHIMMANCIN ZAKKAH

 Hakika Zakkah tana da mutukar muhimmanci domin duk wanda yake fitar da Zakkah kamar yadda Allah ya umarta toh tabbas dukiyar sa Allah zai tsare ta daga masifu irin su: Gobara,asari da kuma mummunar karayar arziki.

  Haka kuma Zakkah tana sa mutune su dinga ganin darajar wanda ya bada ita haka Zakkah tana kawo masalaha tsakanin mai shi da maras shi. Sannan Kuma yadda ake fitar da ita shi ne ka fitar da kashi daya bisa arba'in na dukiyar ka ma'ana zaka kasa dukiyar ka gida arba'in sai ka bada guda daya kachal.

  Mu gane zakkah hakkin Allah Kuma wajibi dole ne ka fitar da ita indai kana so kaga dai-dai a cikin dukiyar ka.

       

Friday, August 28, 2020

MUHIMMANCIN GWAJI KAFIN AURE

 Idan muka duba a da iyaye da kakanni sukan yi aure ba tare da gwaji ba, amma yanzu ya zama wajibi mu gane cewa zamani ya chanza Kuma ilimi na zamani ya yawaita.  Muga ne gwaji kafin aure yanada mutukar muhimmanci don kare iyalin da zaku samu daga cututtuka kamar: Chutar amosanin jini, ciwan hanta da dai sauran chututtuka. Kare kanka da kuma rayuwar iyalin ka.

Wednesday, August 26, 2020

MUHIMMANCIN ILIMIN NAHAWU

 Nahawu na da matukar muhimmancin, duba da irin rawar da ya ke takawa wajen ginin jimla a cikin yare (harshe). Harshe Kuma shi ne babbar alama da ke bambanta mutum da dabba, za mu iya daukar wadannan a matsayin muhimmancin ilimin nahawu;

1. Nazarin kalmomi (tubalan ginin jimla) da ajujuwansu

2. Koyon ka'idojin hada kalmomi don samar da jimla

3. Nazarin karbabbu da illatattun jimloli.d.s.

Tuesday, August 25, 2020

MATASAN AREWA

 Idan muka buba halin da matasa suke ciki na harkar shaye-shaye da kuma sace-sace da kuma sauran munanan dabi'a hali ne wanda yake durkusar da yankin Arewa ta fanni daban- daban Kamar ilimi,tattalin arziki bda Kuma bunkasa cigaban yankunan mu.

  Kamata ya Yi attajiran cikin mu da masu mulkar mu su hada kai domin warware irin wannan matsaloli da matasa ke ciki.

  A duk lokaci da aka ce matashi ya wayi gari ya rasa inda zai je domin samun abun da zai taimaki kansa hakan zai sa ya dinga sake-saken yadda zai samu kudi ko ta halin Yaya hakan zai haifar masa da tinani Mai zurfi harta Kai shi da ya tsinci kansa a shan miyagun kwayoyi.

  Mafita anan idan aka jawo matasa a jiki ana tallafa musu wajan basu jari ko nema musu aiki kamar: Masana'antu,manyan kantina da kuma aikin Gwamnati wannan zai sa hankulan matasa ya kwata Kuma baza su Yi tinanin yin shaye-shaye kokwace da sauran munanan aiyuka. Amma idan aka ce kullum cewa ake a bari amma ba'a yi maganin a bari ba wajan samo wa matasa makoma hakan ni a gurina kamar tukka ake tana warwarewa. 

Shin ina kungiyoyi masu zaman kansu ina majalissar matasa ya kamata ace kun tashi tsaye wajan nemo wa matasa makoma. Allah ya sa mu dace Ameen.

  By Umar Usaini kawo.




INA MUKA DOSA MATASA

 Na dade Ina tuntuntuni akan rayuwar wasu daga cikin matasa idan na tsaya nai tsumm sai na tambayi kaina amma amsar bata zoba wait shin: mat...