Friday, August 28, 2020

MUHIMMANCIN GWAJI KAFIN AURE

 Idan muka duba a da iyaye da kakanni sukan yi aure ba tare da gwaji ba, amma yanzu ya zama wajibi mu gane cewa zamani ya chanza Kuma ilimi na zamani ya yawaita.  Muga ne gwaji kafin aure yanada mutukar muhimmanci don kare iyalin da zaku samu daga cututtuka kamar: Chutar amosanin jini, ciwan hanta da dai sauran chututtuka. Kare kanka da kuma rayuwar iyalin ka.

Wednesday, August 26, 2020

MUHIMMANCIN ILIMIN NAHAWU

 Nahawu na da matukar muhimmancin, duba da irin rawar da ya ke takawa wajen ginin jimla a cikin yare (harshe). Harshe Kuma shi ne babbar alama da ke bambanta mutum da dabba, za mu iya daukar wadannan a matsayin muhimmancin ilimin nahawu;

1. Nazarin kalmomi (tubalan ginin jimla) da ajujuwansu

2. Koyon ka'idojin hada kalmomi don samar da jimla

3. Nazarin karbabbu da illatattun jimloli.d.s.

Tuesday, August 25, 2020

MATASAN AREWA

 Idan muka buba halin da matasa suke ciki na harkar shaye-shaye da kuma sace-sace da kuma sauran munanan dabi'a hali ne wanda yake durkusar da yankin Arewa ta fanni daban- daban Kamar ilimi,tattalin arziki bda Kuma bunkasa cigaban yankunan mu.

  Kamata ya Yi attajiran cikin mu da masu mulkar mu su hada kai domin warware irin wannan matsaloli da matasa ke ciki.

  A duk lokaci da aka ce matashi ya wayi gari ya rasa inda zai je domin samun abun da zai taimaki kansa hakan zai sa ya dinga sake-saken yadda zai samu kudi ko ta halin Yaya hakan zai haifar masa da tinani Mai zurfi harta Kai shi da ya tsinci kansa a shan miyagun kwayoyi.

  Mafita anan idan aka jawo matasa a jiki ana tallafa musu wajan basu jari ko nema musu aiki kamar: Masana'antu,manyan kantina da kuma aikin Gwamnati wannan zai sa hankulan matasa ya kwata Kuma baza su Yi tinanin yin shaye-shaye kokwace da sauran munanan aiyuka. Amma idan aka ce kullum cewa ake a bari amma ba'a yi maganin a bari ba wajan samo wa matasa makoma hakan ni a gurina kamar tukka ake tana warwarewa. 

Shin ina kungiyoyi masu zaman kansu ina majalissar matasa ya kamata ace kun tashi tsaye wajan nemo wa matasa makoma. Allah ya sa mu dace Ameen.

  By Umar Usaini kawo.




Sunday, August 23, 2020

Ma'anar amsa-amo(kafiya)

 Amsa-amo na nufin harafin baidaya dake  karshen layin waka.

Misali:

Kwaya idan aka sha ta tana bugarwa ta kaika kwata

Daganan ka gane baka komai sai warin kwata.


Hanyoyi goma Dan magance matsalar rashin aikin Yi a Arewa

 1-Hadinkan dattawan Arewa  su tafi da murya daya don Samar wa matasa makoma daga gwamnati.

2-Samar da masana'antu domin cigaban matasa daga wurin attajirai.

3-Dukkan wata masana'anta da aka bude ko bamban kanti ya kasan ce kashi chasa'in y'an Arewa ne suke aiki a cikin sa.

4-Samarda kungiyoyin sakai a unguwanni domin tattara taimako don samawa matasa aikin Yi.

5-Hadinkan matasa don taimakonka juna a tsakanin su.

6-Cire sankai wajan bawa wanda ya suka dace a taimakonkawa don yin sana'o'i.

7-Fitar da Zakkah ga attajirai kuma su bawa wanda ya kamata bisa shari'a.

8-Kowanne attajirin unguwa ya kasan ce ya samar wa matasa aikin yi ko jari a cikin unguwar sa.

9-Samar da wuraren yin sana'o'in hannu daga gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kansu.

10-Gwamnati ta samar da hanyoyin da masu sana'o'i wajan saida kayan su cikin sauki.

        By Umar Usaini 📝

INA MUKA DOSA MATASA

 Na dade Ina tuntuntuni akan rayuwar wasu daga cikin matasa idan na tsaya nai tsumm sai na tambayi kaina amma amsar bata zoba wait shin: mat...